Wani jirgin kasar Kenya makare da fasinjoji ya yi batar dabo

Wani jirgin kasar Kenya makare da fasinjoji ya yi batar dabo

An dakatar da neman wani karamin jirgin saman fasinjoji da ya bace a yammacin Talata a Kenya a daren jiya Talata sai dai za'a cigaba da neman da asubahin yau.

Jirgin saman ya tashi ne daga Kitale, wani birni da ke yammacin Kenya a hanyar zuwa filin tashin jirage na kasa da kasa na Jomo Kenyatta da ke Nairabi babban birnin Kenya, kamar yadda Hukumar Kula da harkokin jiragen sama na Kenya (KCAA) ta ce.

Wani jirgin saman Kenya dauke da fasinjoji ya bace

Wani jirgin saman Kenya dauke da fasinjoji ya bace

Jirgin na dauke da fasinjoji takwas ne da kuma ma'aikatan jirgi biyu kamar yadda wata sanarwa da kamfanin Fly Sax ta bayyana a shafinta na yanar gizo.

KU KARANTA: Kada ya cinye wani fasto yayin da yake yi wa mabiyansa wankan tsarki a kogi

"Tuni an baza masu bincike da taimakon gaggawa amma har zuwa yammacin jiya Talata ba'a gano inda jirgin ya ke ba.

"An dakatar da neman saboda dare ya yi amma za'a cigaba da safe," inji KCAA.

A wata rahoton kuma, Legit.ng ta kawo muku labarin inda wasu mazauna kauye a jihar Filato suka kaiwa shanun makiyaya hari inda suka kashe guda 38, kana suka raunata 15.

Rundunar Operation Safe Haven da ke jihar sun kaiwa makiyayan dauki, sun kuma fara gudanar da bincike tare da sauran jami'an tsaro da ke yankin har ma da masu sarautun gargajiya don binciko wadanda suka aikata wannan ta'asa.

Shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah ya yi zargin cewa matasan Birom ne suka kai harin duk da ya ke jami'an tsaro basu tabbatar da hakan ba har sai an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel