Mataimakin shugaban kasa baiyi umurnin sallaman kowani jami’i daga ofishin amnesty ba – Fadar shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa baiyi umurnin sallaman kowani jami’i daga ofishin amnesty ba – Fadar shugaban kasa

Ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo bata yi umurnin dakatar da wani ma’aikaci daga ofishin amnesty ba, mai ba shugaban kasa shawara akan lamuran Niger Delta, Farfesa Charles Dokubo ya bayyana.

Farfesa Dokubo a wata sanarwa day a saki a ranar Talata ya bayyana cewa an janyo hankalinsa ga wani rahoton cewa “wata mata ta rasa aikinta bayan ta soki mataimakin shugaban kasa a yanar gizo”.

Wani rahoto da aridar Premium Times ta wallafa yayi zargin cewa wata Ms Bolouere Opukiri tayi ikirarin ta rasa aikinta satinta na farko da fara aiki.

Mataimakin shugaban kasa baiyi umurnin sallaman kowani jami’i daga ofishin amnesty ba – Fadar shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa baiyi umurnin sallaman kowani jami’i daga ofishin amnesty ba – Fadar shugaban kasa

Tayi zargin cewa farfesa Dokubo ya bukaci a koreta a lokacin day a ziyarci fadar shugaban kasa a farkon watan Mayu ta kara da cewa sun fada masa cewa suna sane da sake dawo da ita don haka a koreta kada ta sake sabawa fadar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Dahiru Bauchi ya yi bude baki da ministan matasa da wasanni (hotuna)

Don haka Farfesa Dokubo ya karyata rahoton inda ya bayyana hakan a matsayin makircin magauta da kuma sharri.

Yace babu wani umurni makamancin haka daga ofishin mataimakin shugaban kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel