Mazauna wani kauye a Filato sunyi wa makiyaya mummunar ta'asa

Mazauna wani kauye a Filato sunyi wa makiyaya mummunar ta'asa

- Mazauna wata kauye a jihar Filato sun yiwa makiyaya mumunanr ta'addi

- Sun kashe shanu 38 tare da yiwa wasu 15 mummunan rauni

- Rundunar soji na Operation Safe Haven sun tabbatar da afkuwar lamarin kuma suna kokarin gano wanda auka aikata ta'asar

A kalla shanu guda 38 mallakar makiyaya ne mazauna kauyen Tanjol da ke karamar hukumar Riyom na jihar Filato suka harbe a ranar a jiya Litinin.

An kashe shanu 38, an kuma jikkata wasu 15 a jihar Filato

An kashe shanu 38, an kuma jikkata wasu 15 a jihar Filato

KU KARANTA: Jihohin Najeriya 10 da ke gaba a yawan masana'antu

Daily Trust ta gano cewa an kuma raunata wasu shanun 15 da harsashai da kuma sarar adduna wanda hakan ya sanya masu shanun dole suka yanka su, jami'an tsaro na safe Operation Safe Haven sun taimakawa makiyayan daukan shanun.

Shugaban matasa na kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah na kasa (MACBAN), Ibrahim Yusuf ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa matasan Berom ne suka kashe shanun, ya kara da cewa "lokacin da makiyayan suka iso inda abin ya faru tare da jami'an Safe Haven don su yanka shanun da aka yi wa rauni, matasan sun sake bude musu wuta."

Jami'in hulda da jama'a na Operation Safe Haven, Manjo Adam Umar, ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai bayar da adadin shanun da aka kashe da kuma wanda aka raunata ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel