Miyagun mutane sun yi ma wata daliba fyade sa’nnan suka yi ma kisan gilla

Miyagun mutane sun yi ma wata daliba fyade sa’nnan suka yi ma kisan gilla

Wata daliba a kwalejin koyon ilimin jinya dake garin Jalingo na jihar Taraba, Mercy Victor ta gamu da ajalinta a hannun wasu miyagun mutane a daren Lahadi, 3 ga watan Yuni, yayin da take kan hanyarta ta zuwa makaranta, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar mutanen suna tare Mercy ne a gab da babban asibitin Jalingo, inda suka yi mata fyaden taron dangi, suka tara mata gajiya, daga bisani kuma suka caccaka mata wuka, sa’annan suka jefar da gawarta a daji.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya tsige Buhari matukar ina raye – Inji Gudaji Kazaure

Kaakakin rundunar Yansandan jiha Taraba, David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace: “An kawo mana rahoto kan abinda ya faru da Mercy, amma sai aka mayar da karar zuwa Ofishin Yansanda dake GRA don cigaba da gudanar da bincike.”

Shima shugaban dalibai yan asalin jihar Taraba, Hope Vyonku ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace wani mutumin kirki ne ya tsinci Mercy kwance jike da jinni sharkaf, inda yayi gaggawar garzayawa da ita zuwa Asibiti, ta cika da safiyar Litinin.

Hope yayi kira ga Yansanda da su dage kaimi wajen gano wadanda suka tafka wannan ta’asa, sa’annan yayi kira ga dukkanin hukumomin tsaro dake jihar dasu tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar musamman dalibai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel