Zaben 2019: Kuri’ar Talakawa za tayi aiki ba magudi ba inji Hukumar zabe

Zaben 2019: Kuri’ar Talakawa za tayi aiki ba magudi ba inji Hukumar zabe

- Hukumar INEC tace babu wanda zai iya murde zabe mai zuwa na 2019

- INEC tace fasahar zamanin da aka kawo a zaben 2015 ya gyara lamarin

- Hukumar zaben tayi watsi da kukan da PDP ke yi na cewa ana murdiya

Mun samu labari cewa jiya ne wani babban Jami’in Hukumar zabe na Kasa watau INEC ya cika-baki inda yace ba zai yiwu a murde zabe yanzu a Najeriya ba saboda gyare-gyaren da aka kawo.

Zaben 2019: Kuri’ar Talakawa za tayi aiki ba magudi ba inji Hukumar zabe

Hukumar INEC tace a zaben 2019 babu maganar murdiya

Wannan babban Jami’i na Hukumar zaben na kasa yayi watsi da koke-koken da Jam’iyyar adawa ta PDP ke yi na cewa sai yadda fadar Shugaban Kasa Buhari tayi da Hukumar. Jami’in na INEC yace sam babu kanshin gaskiya a wannan maganar na PDP.

KU KARANTA: Dole Jama’a su hada-kai domin a taimakawa Shugaba Buhari – Lawan

INEC tace ta gudanar da zabuka dabam-dabam bayan zaben 2015 kuma Jam’iyyar PDP tayi nasara a da-dama daga cikin su don haka maganar ace ana hada baki tsakanin Hukumar zaben na INEC da Jam’iyyar APC mai mulki ba gaskiya bane.

Haka kuma Hukumar zaben na kasa tace fasahar da aka kawo na zamani ya bada damar al’umma su zabi wanda su ke so. Fasahar da aka kawo a 2015 dai na tantance masu kada kuri’a shi ne yayi maganin makudin da ake yi a zabe inji INEC.

Sai dai INEC tace ba za a sake kirkirar wasu tashoshin zabe ba daga nan har 2019 domin kuwa yin hakan zai kara kawo matsala ne kurum. Sai dai kuma za a raba wasu wuraren zaben gida 2 a kara yawan akwatin zabe domin a rage cinkoso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel