Wani Sabon Harin 'Yan Bindiga ya salwantar da Rayuka 5 a Jihar Taraba

Wani Sabon Harin 'Yan Bindiga ya salwantar da Rayuka 5 a Jihar Taraba

Hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta bayyana cewa, rayukan mutane biyar sun salwanta tare da raunatar da dama a wani sabon harin 'yan Bindiga da ya afku a Kauyukan Dan-Anacha da Dinya dake karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP David Missal, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai da ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun kai wannan mummunan hari ne a daren ranar Litinin din da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, a yayin wannan hari 'yan Bindigar sun kuma kone wasu gidaje a kauyukan wanda a sanadiyar hakan ne suka salwantar da rayukan mutane biyar.

Wani Sabon Harin 'Yan Bindiga ya salwantar da Rayuka 5 a Jihar Taraba

Wani Sabon Harin 'Yan Bindiga ya salwantar da Rayuka 5 a Jihar Taraba

ASP Missal yake cewa, jami'an tsaro sun garzaya wannan kauyuka da harin ya afku inda suka taki rashin sa'a yayin isar su da Maharan suka tsere da sai kwara guda cikin su da ashe karar kwana ta kawo shi.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya na Zukar Karan Sigari Biliyan 20 a Shekara - Ministan Lafiya

Ya kara da cewa, tuni tarzoma ta lafa a yankunan yayin da al'umma suka ci gaba da gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali sakamakon jami'an tsaro da suka mamaye ko wane lungu da sako.

Shugaban karamar hukumar ta Gassol, Alhaji Yahuza Ya'u, ya tabbatar da afkuwar wannan hari inda ya ce sun gudanar da wani taron Tsaro na gaggawa dangane da lamarin tare da dukkanin masu ruwa da tsaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel