Wani tsoho mai shekaru 70 ya mutu yayin wata turereniya a sansanin ‘yan gudun hajira a Maiduguri

Wani tsoho mai shekaru 70 ya mutu yayin wata turereniya a sansanin ‘yan gudun hajira a Maiduguri

Wani tsoho mai shekaru 70 ya mutu yayin da wasu mutane biyu suka samu raunuka a wata turereniyar karbar abincin bude baki a sansanin ‘yan gudun hijira dake Maiduguri, jihar Borno.

Yabawa Kolo, shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Borno (SEMA), ta sanar da hakan yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai a yau, Talata.

Kolo ta bayyana cewar tsohon ya mutu ne yayin da mazauna sansanin gudun hijirar ke turereniyar karbar abincin bude baki a sansani El-Miskin yayin da mutane biyu suka samu raunuka a sansanin Madinatu, dukkan su a cikin garin Maiduguri.

Wani tsoho mai shekaru 70 ya mutu yayin wata turereniya a sansanin ‘yan gudun hajira a Maiduguri

Sansanin ‘yan gudun hajira a Maiduguri

Kazalika ta bukaci masu kawo agaji ga mazauna sansanin gudun hijirar das u ke girmama dokokin da hukuma ta saka domin kare lafiyar su.

DUBA WANNAN: Wata yarinya ta dawo gida shekaru biyu bayan mutuwar ta, an samu itatuwa bayan an tona kabarin ta

“SEMA na rokon jama’a masu kawo taimako da kungiyoyin agaji da basu da dabarun sarrafa taron jama’a das u nemi taimakon jami’an mu dake da kwarewa yayin da zasu raba kayayyaki ga mazauna sansanin ‘yan gudun hijira,” a cewar Kolo.

Kolo t ace hukumar SEMA ba zata ji nauyin daukan matakan shari’a a kan duk kungiya ko wani mutum da ya haddasa rudani ko haifar da lahani ga ‘yan gudun hijirar ba yayin rabon kayan agaji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel