Ba bu Hannun Osinbajo wajen bayar da Umarnin Sallamar Ma'aikaciyar Amnesty - Fadar Shugaban Kasa

Ba bu Hannun Osinbajo wajen bayar da Umarnin Sallamar Ma'aikaciyar Amnesty - Fadar Shugaban Kasa

Ofishin Mataimakin shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tsarkake ubangidan sa daga sanya hannu cikin sallamar wata ma'aikaciyar fadar shugaban Kasa da ta soki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.

A makon da ya gabata ne shafin jaridar Premium Times ya ruwaito cewa, an sallami wata ma'aikaciyar ofishin mataimakin shugaban kasa, Bolouere Opukiri, a dalilin sukar Osinbajo da ta sakamakon ficewa daga kasa yayin da yake mukaddashin shugaban kasa ba.

Jaridar ta ruwaito cewa, cikin rubutacciyar sukar da ta yiwa mataimakin shugaban kasa a shafin ta na sada zumunta da cewar ya aikata ba daidai ba na barin kasar nan kasancewar sa mukaddashin shugaban kasa a yayin da shugaba Buhari ke jinya a kasar Birtaniya.

Rahotanni sun bayyana cewa, ba ya ga sukar mataimakin shugaban kasa, Misis Opukiri ta kuma soki uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, da cewar ko kusa ba ta kusanto Dame Patience Jonathan, Uwargidan tsohon shugaban kasa Jonathan ta fuskar aji da wayewa ba.

Ba bu Hannun Osinbajo wajen bayar da Umarnin Sallamar Ma'aikaciyar Amnesty - Fadar Shugaban Kasa

Ba bu Hannun Osinbajo wajen bayar da Umarnin Sallamar Ma'aikaciyar Amnesty - Fadar Shugaban Kasa

A yayin mayar da martani dangane da tuhumar fadar shugaban kasa akan sallamar wannan ma'aikaciya daga bakin aikin ta, ofishin mataimakin shugaban kasa reshen shirin Amnesty ya tsarkake kansa daga wannan zance na shaci fadi da kuma kage.

Da sanadin mai bayar da shawara ta musamman ga mataimakin shugaban kasa akan harkokin da suka shafi yankin Neja Delta, Farfesa Charles Dokubo ya bayyana cewa, ko kadan wannan zantuka ne na shaci fadi da kuma kage dake neman janyo hankalin al'umma da kuma bayar da mummunar manufa.

KARANTA KUMA: Yara 152m ke Aikin 'Kwadago duk Shekara a fadin Duniya - ILO

Yake cewa, ko kadan ofishin mataimakin shugaban kasa ba ya da wata shaida da ta ke bayyana Misis Opukiri a matsayin ma'aikaciya ko kuma wadda take kan wani kwantiragi na aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa ballantana ya kai ga har an sallame ta daga bakin aiki.

A sanadiyar hake ne Farfesa Dokubo yake kiran al'umma akan su yi watsi da wannan babatu na Misis Opukiri da cewar kazafi ne take neman yiwa fadar shugaban kasa domin cimma wata manufa, inda yake cewa ba taba kasancewa ma'aikaciya a fadar ba ballantana ta kai ga sallamar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel