Makiyaya sun tafka mummunar barna a jihar Nassarawa har da kashe jami’an tsaro 3

Makiyaya sun tafka mummunar barna a jihar Nassarawa har da kashe jami’an tsaro 3

- Har yanzu bata sauya zani ba dangane da matsalar rikicin Makiyaya a kasar nan

- A harin baya-bayan nan wasu Makiyayan sun hallaka jami'an 'Yan sanda

A ƙalla jami'an rayukan ‘Yan sanda uku ne da jami'an sashin manyan laifuka (SARS) da kuma karin wasu Mutane Takwas ne suka salwanta daga hannun Makiyaya Fulani a Mararaba Udege da Aisa da kuma Aguma na karamar hukumar Nassarawa dake Jihar Nasarawa.

Wannan al'amari ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata inda harin yayi sanadiyyar lalata gidaje da dama da kuma dukiyoyin al'umma.

Makiyaya sun tafka mummunar barna a jihar Nassarawa har da kashe jami’an tsaro 3

Makiyaya sun tafka mummunar barna a jihar Nassarawa har da kashe jami’an tsaro 3

Majiyarmu dai ta waito cewa jami'an ‘Yan sandan da suka mutu an tura su yankin ne domin yin sulhu a tsakanin kabilar Agatu da Kuma Makiyayan, wanda aka far musu har ajali yayi halinsa.

Kakakin hukumar ‘Yan sanda na jihar Ismaila Usman ya tabbatar da faruwar wannan lamari a yau talata a garin Lafia.

KU KARANTA: Tsautsayi: Harin ‘yan Boko Haram ya kashe Mutane 9

Lamarin ya faru ne bayan da wani Bafulatani ya kashe mutumin Agatu kuma yayi awon-gaba da babur din hawansa.

Usman ya ce "Bayan da muka samu labarin hare-hare da Fulanin suka kai sai muka tashi jami'anmu domin zuwa su kawo karshen hatsaniyar da kuma daidaita komai a yankin, amma kawai sai aka farwa jami'anmu suka kashe su".

Kamar yadda ya bayyana wanda suka rasa rayukansu sun hada da jami'i mai mukamin Sufeto da sajan da kuma mai mukamin kofural. A cewar Kakakin

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel