Zakaran da Allah ya nufa da Cara: Cikakken jerin sunayen shuwagabannin APC na jihohi 36

Zakaran da Allah ya nufa da Cara: Cikakken jerin sunayen shuwagabannin APC na jihohi 36

Daga karshe dai bayan an kammala hada hadar bani gishiri in baka manda irin na siyasa, jam’iyyar APC ta fitar da sunayen sabbin shuwagabanninta a matakin jiha, na jihohin Talatin da shida, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai rahoton ya nuna cewa ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun kwashi kashinsu a hannu, bayan da uwar jam’iyyar ta yi watsi da sunayen da suka mika mata da sunan sune shuwagabannin jam’iyyar a jaha.

KU KARANTA: Ba cas ba as! Wani Uba ya caka ma Diyarsa wuka yayin da take barci

Ministocin sun hada da ministan watsa labaru, Lai Muhammed da na sadarwa, Adebayo Shittu, inda a jihar Kwara, uwar APC ta yi watsi da sunan Moshood Bolarinwa da Lai ya mika mata, haka nan ta yi watsi da Isiaka Alimi, wanda Shittu ya mika mata.

Ga jerin sunayen nan kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito:

Abia- Donatus Nwankpa

Adamawa- Ibrahim Bilal

Akwa Ibom- Ini Okopido

Anambra- Emeka Ibe

Bauchi- Uba Ahmed Nana

Bayelsa- Jonathan Amos

Benue- Abba Yari

Borno- Ali Dalori

Cross River- Godwin John

Delta- Cyril Ogodo

Ebonyi- Eze Nwachukwu

Edo- Anslem Ojezua

Ekiti- No Congress

Enugu- Ben Nwoye

Gombe Nitte Amangal

Imo- Hillary Eke

Jigawa- Ado Sani Kiri

Kaduna- Emmanuel Jekeda

Kano- Abdullahi Abass

Katsina- Shittu Shittu

Kebbi – Bala Sani Kangiwa

Kogi- Abdullahi Bello

Kwara- Ishola Balogun Fulani

Lagos- Tunde Balogun

Nasarawa- Philip Shekwo

Niger- Muhammed Liman

Ogun- Dikia Adebisi

Ondo- Ade Adetimehin

Osun- No Congress

Oyo- Akin Oke

Plateau- Letep Dabang

Rivers- Ojukaye Amachree

Sokoto- Isa Achida

Taraba- Abdulmumini Vaki

Yobe- Adamu Chilariye

Zamfara- Lawal Liman and

FCT Abuja- Abdulmalik Usman

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel