Rana ta kwacewa wasu ‘yan fashi sun shiga hannun Kuliya basu ji da dadi ba

Rana ta kwacewa wasu ‘yan fashi sun shiga hannun Kuliya basu ji da dadi ba

- Wasu 'yan Fashi da Makami sun shiga hannu, har an gurfanar da su gaban Kotu

- Bayan sauraren karar, mai shari'ar ya infiza keyarsu gidan kaso

A ranar talata ne wata kotu dake zamanta a Ibadan ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin zaman gidan kaso a bisa zarginsu da ake da yin fashi-da-makami, wato Segun Oke da kuma Taye Bolaji.

Mai shari'ar kotun Laniran Akintola ta tisa keyar wadanda ake tuhumar ne zuwa gidan kaso duk kuwa da cewa sun musanta zargin da ake a kansu.

Rana ta kwacewa wasu ‘yan fashi sun shiga hannun Kuliya basu ji da dadi ba

Rana ta kwacewa wasu ‘yan fashi sun shiga hannun Kuliya basu ji da dadi ba
Source: UGC

Yanzu haka dai mai Shari'a Akintola ta dage zaman har sai ranar 25 ga watan Satumba sannan za a dawo domin cigaba da sauraren karar.

Lauyan dake kare wanda aka yi wa fashin, Kahinde Adeleye ya bayyanawa kotu cewar ana tuhumar su biyun ne bisa laifin fashi da makami sannan ana zarginsu da mallakar muggan makamai.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya na Zukar Karan Sigari Biliyan 20 a Shekara - Ministan Lafiya

Ya ce 'yan fashin sun kwaci wayoyin hannu da Na'urar komfuta da sauran kayayyaki wanda darajarsu ta kai Naira 643,000. Ya ce fashi da makamin ya faru ne a unguwar Adegbayi a garin Ibadan da misalin karfe 2:00am na dare a ranar 28 ga watan Mayun shekara ta 2015.

A cewarsa wannan laifi ne da ya sabawa kudin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 2000, a ƙarƙashin sashi na 2(a) da (b) cikin baka na laifukan fashi da makami.

Sai dai lauyan dake kare wanda ake tuhumar ta bukaci kotun da a ɗage zaman Kotun zuwa nan gaba da kuma bayar da damar yin belin wadanda ake zargin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel