Ba cas ba as! Wani Uba ya caka ma Diyarsa wuka yayin da take barci

Ba cas ba as! Wani Uba ya caka ma Diyarsa wuka yayin da take barci

Jami’an rundunar Yansandan jihar Anambra sun tabbatar da kama wani Magidanci mai shekaru 60, Cletus Aguluka da ya hallama diyarsa, yar budurwa babu cas ba as, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari mai tsananin muni ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe biyu na dare a gidansu dake kauyen Awgbu, cikin karamar hukumar Orumbo ta Arewa na jihar.

KU KARANTA: Ga Buhari ga Atiku: Ministan Buhari ta yi tsayuwar gwamen Jaki

Mahaifiyar budurwar mai suna Georgia Aguluka ta bayyana cewa sun shiga cikin tashin hankali tun bayan da Maigidan nata ya dawo gida cikin maye sakamakon giya da ya sha yayi tatil.

Uwargida Georgina ta bayyana cewa yana cikin halin mayen ne sai yazo yana neman fitilarsa don ya haska, amma ya nema ya rasa, daga nan ne kawai sai ya fara zage zage, inda ya dauki wuka ya burma m diyarsa dake kwance tana barci a dakin.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace zasu mika wanda ake tuhumar gaban Yansanda da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel