Ana jan kafa kan shari'ar wani dan Amurka da ya damfari 'yan Najeriya $565,000

Ana jan kafa kan shari'ar wani dan Amurka da ya damfari 'yan Najeriya $565,000

Rashin bayyanar lauya mai kare Marco Ramirez, wani da Amurka da ake tuhuma da laifin damfarar yan Najeriya gudu uku kudi $565,000 don samar musu takardar izinin zama a kasar Amurka ya fuskanci tsaiko a babban kotun Ikeja.

A ranar 22 ga watan Yunin 2017 ne hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da Ramirez a gaban kotu inda ake tuhumar sa da aikata laifuka 16 masu alaka da damfarar kudi.

Ya ki amincewa da tuhumar da ake masa hakan yasa Alkali Josephine Oyefeso ta bayar da belinsa a kan kudi $250,000 tare da masu tsaya masa guda biyu a ranar 10 ga watan Yuli na shekarar 2017.

Ana jan kafa kan shari'ar wani dan Amurka da ya damfari 'yan Najeriya $565,000

Ana jan kafa kan shari'ar wani dan Amurka da ya damfari 'yan Najeriya $565,000

KU KARANTA: Talauci ya sanya na sayar da jariri na kan kudi N670,000 - Wata matashiya 'yar shekaru 17

Da aka fara sauraron karar a yau Talata, Ramirez bayan cika ka'idojin belinsa ya shaidawa kotu cewa bashi da lauyan da zai kare shi.

"Bani da lauyan da zai kare ni domin a safiyar yau na nemi lauyan na a wayansa amma ban same shi ba," inji shi.

A bangarensa, lauyan mai shigar da kara na hukumar EFCC, V.O. Agbaje ya bukaci kotun ta sake sanya sabbon ranar da za'a saurari karar.

Alkalin kotun, Justice Oyefeso ya amince da bukatar lauyan EFCC inda ya dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni inda lauyoyin biyu za su sake amincewa a kan sabuwar ranar da za'a cigaba da shari'ar.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa gwamnatin kasar Amurka ta yankewa Ramirez hukunci kan laifukan damfara da wasu masu kama da hakan duk da cewa baya kasar.

A cewar EFCC, Ramirez ya karbi $545,000 daga hannun Amb. Godson Echejue don saka hannun jari a kamfaninsa ya kuma karba $10,000 daga hannun wani Abubakar Umar sai kuma ya karbi $10,000 daga Olukayide Sodimu don samar musu takardan izinin zama a Amurka na dundundun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel