Ba laifi bane shugaba ya wawuri kudin Gwamnnati har a wajen Allah – Gumi

Ba laifi bane shugaba ya wawuri kudin Gwamnnati har a wajen Allah – Gumi

Fitaccen Malamin addininnan na jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bara a yayin gudanar da tafsirin Al-Qur’ani da yake yi a Masallacin Sultan Bello, inda yace babu laifi idan har shugaba Musulmi ya tabbatar da Shari’ar Musulunci ya debi kudin Al’umma yayi wadaka, har a wajen Allah.

Legit.ng ta jiyo Gumi cikin wani bidiyo yana wanke tsofaffin gwamnanonin jihohin Kano, Sakkwato da Zamafar daga aikata duk wani badakalar kudi, inda yace tunda har sun kawar da ayyukan zinace zinace da shaye shaye ta hanyar fatattakar gidajen karuwa da na giya, kamata yayi Musulmai su rufa musu asiri.

KU KARANTA: Wata Annoba ta hallaka daliba 1, ta kwantar da 40 a kwalejin yan Mata na Kaduna

“Da garuruwanmu daga gidan Karuwai sai gida Giya, amma yanzu akwai su a Zamfara, Kano da Sakkawato? Sai dai a yi a boye, wannan gyaran da mutanen suka yi ko sun yi mu suturtasu, domin sun dawo da darajar addinin Musulunci da shari’ar Musulunci.

“Ambaton mutanen da aibi kansa babban aibi ne, balle ace wai sun saci naira biliyan daya, ba biliyan daya ba, kamata yayi kamar yadda aka yi ma shugaban kungiyar Kiristoci muma Musulmai mu hada kudi mu sayi jirgin sama mu baiwa tsohon gwamnan Zamfara, Yarima ya dinga hawa yana shawagi.” Inji Gumi.

Malamin ya soki gwmanati, inda yace gwamnatin Buhari bata san shari’a ba, don haka ta gurfanar da shi gaban Kotu, haka zalika yace duk abinda Shekarau yayi bai kamata Muusulmai su bari a ci mutuncinsa ba, “Da ba dan mun tsawata akan maganan Ramalan ba, da wata rana an daura ma Shekarau laifukan da yayi akan allo a kirjinsa.”

Malam bai karkare bayaninsa ba sai ya halasta ma shuwagabanni ire iren Shekarau kudaden baitil Malin gwamnati, inda yace “Kudaden da suka ci basu da laifi a wajen Allah ko kadan, zamu tattauna maganan Dukiya a cikin suratul Anfal.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel