'Yan Najeriya na Zukar Karan Sigari Biliyan 20 a Shekara - Ministan Lafiya

'Yan Najeriya na Zukar Karan Sigari Biliyan 20 a Shekara - Ministan Lafiya

Ministan Lafiya na Najeriya, Farfesa Isaac Adewole ya bayyana cewa ana amfani da sama da Karan Sigari Biliyan 20 cikin kowace Shekara a fadin Kasar nan.

Farfesa Adewole ya bayyana cewa akwai kimani mutane miliyan 4.5 dake ta'ammali da Sigari a fadin Najeriya yayin da kimanin kaso 89 cikin 100 masu ziyartar gidajen rawa suke fama da barazanar illolin Sigari ba tare da sun yi amfani da ita ba.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai domin murnar tunawa da ranar yin hattara da Sigari da aka gudanar a babban Birnin Kasar nan na Abuja a ranar Litinin din da ta gabata.

Ministan Lafiya; Farfesa Isaac Adewole

Ministan Lafiya; Farfesa Isaac Adewole

Yake cewa, kididdigar da aka fitar a shekarar 2015 ya bayyana yadda Kasar Najeriya ke tafka asara ta Dalar Amurka Biliyan 7.6 a sanadiyar masu almubazzaranci na ta'ammali da Karan Sigari.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, Legit.ng ta fahimci cewa ana gudanar da biki na murnar tunawa da wannan rana ta yin hattara da Sigari a ranar 31 ga watan Mayun na kowace shekara.

KARANTA KUMA: Wata Mata ta Kashe Mijin ta daga yiwa Kyanwar su Duka

Ya ci gaba da cewa, ta'ammali da Sigari a kasar nan shi ke sanadiyar tabarbarewar tattalin arziki a bangaren Kiwon Lafiya, inda hasashe ya bayyana yadda ake tafka asara ta kimanin Dalar Amurka Miliyan 800 a sakamakon cututtukan Zuciya da na Sukari da Sigari ke haddasawa al'ummar Najeriya.

Ya kara da cewa, cikin kowane jari na $1 da aka sanya cikin kasuwancin Sigari, akwai kimanin $3 da ake barnatarwa wajen Kiwon lafiya, inda yake cewa kamfanonin Sigari su na samun riba mai yawan gaske ba tare da daukar alhaki da nauyi na lahanin da suke haifarwa al'umma ba.

A yayin fashin baki dangane da sabuwar hanyar zuke-zuke ta zamani mai sunan Shisha da ta shahara cikin Matasan Kasar nan, Farfesa Adewole ya bayyana cewa, kasar Najeriya ba za ta lamunci duk wata basaja ta ta'ammali da sunadarin Tobacco domin kare makomar Kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel