Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da shugabannin tsaro a cikin Aso Rock

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da shugabannin tsaro a cikin Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro cikin sirri a ranar Talata, 5 ga watan Yuni.

A lokacin wannan rahoton an tattaro cewa ana ganawar ne a fadar shugaban kasa dake Abuja, babban birnin tarayya.

“Wadanda suka halarci ganawar sune babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Mohammed Babagana Monguno, ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, darakta janar na hukumar liken asiri ta kasa NIA, Ahmed Abubakar, da kuma Sufeto Janar na yan Sanda, Ibrahim Idris.

KU KARANTA KUMA: Anci zarafin addinin Musulunci a wakar Shaku Shaku – MURIC

“Hakan ya biyo bayan wata ganawa da sukayi a ranar Litinin, 4 ga watan Yuni inda shugaba Buhari da Osinbajo sukayi ganawa daban-daban da shugabannin tsaron,” cewar rahoton.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel