Tsautsayi: Harin ‘yan Boko Haram ya kashe Mutane 9 a Nijar

Tsautsayi: Harin ‘yan Boko Haram ya kashe Mutane 9 a Nijar

- Kwanan wasu Mutane ya kare sanadiyyar harin da 'yan kunar bakin wake suka kai

- Harin dai an kai shi ne gab da gabar Najeriya da Nijar a garin Diffa

- Hare-haren 'yan Boko Haram dai ya ja baya sakamakon jajircewar Sojojin Najeriya da kuma Rundunar hadaka

Mahukunta sun bayyana cewa a kalla Mutane Tara ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai garin Diffa dake kudancin kasar Nijar.

Tsautsayi: Harin ‘yan Boko Haram ya kashe Mutane 9

Tsautsayi: Harin ‘yan Boko Haram ya kashe Mutane 9

A cewarsu harin ya faru ne bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake a kimanin su uku suka tayar da bam din dake jikinsu a wurare daban-daban na garin Diffan.

Garin na diffa ya sha fama da aiyukan ‘yan tada kayar bayan na Boko Haram kasancewarsa yana makwabtaka da Najeriya.

KU KARANTA: Ya kamata yan Najeriya su nemi sanin kudaden da ake kashewa Gwamnoni da shugaban kasa – Shehu Sani

An dai dade ba’a samu bullar ‘yan Boko Haram ko kai hari yankin na Diffa ba tun bayan da aka kafa rundunar Sojojin hadaka da suka kunshi Sojoji daga kasar Chadi da Nijar da Kamaru da kuma Najeriya.

Bisa yawaitar hare-haren da ake kai masa ne ya sanya aka kakabawa garin dokar ta baci a shekara ta 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel