IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

Yanzun nan, mambobin majalisan wakilan tarayya da na dattawa sun shiga ganawar gaggawa domin tattauna bita da kullin siyasa da ake wa mambobinsu a kasan nan.

Wannan shine sakamakon ganawar da suka yi ranan Litinin na samun mafita daga cikin wannan zalunci da kama karyan da akewa shugabanninsu.

A ranan Lahadi, Jami'an 'Yan Sandan Najeriya sun gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki ya hallara a gaban su kan wani fashi da aka yi kwanaki a Jihar Kwara domin ya wanke sa.

Idan ba ku manta ba dai kwanaki ne aka yi wani mummunan fashi da makami a wani banki a Garin Offa da ke cikin Jihar Kwara. Ana zargin cewa akwai sa hannun Shugaban Majalisar Tarayyan a wajen wannan danyen aiki.

IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

IGP Idris: Yan majalisan dokokin tarayya sun shiga ganawar gaggawa

Mutum 15 da ake tunanin da su aka yi wannan fashi sun shiga hannun Jami’an tsaro. Ana zargin cewa wasun su su na yi wa Bukola Saraki aiki tun lokacin yana Gwamnan Jihar Kwara. A 2007 ne Saraki ya bar Gwamna ya zama Sanata.

KU KARANTA: Ana tsananin fama da duhu a Garin Shugaban Kasa Buhari

An dai kashe mutane sama da 30 lokacin da aka yi wannan fashi daga ciki har da wasu mata masu juna-biyu. Daya daga cikin ‘Yan fashin yace ba Bukola Saraki ya tura su wannan aiki ba amma dai tabbas ya san da zaman su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel