An tallafawa 'Yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar Kano da kudi har N1.3bn

An tallafawa 'Yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar Kano da kudi har N1.3bn

- Lokacin darawar wadanda iftila'in Gobara ya rutsa da kayansu a Kano ya zo

- Mukaddashin Gwamnan jihar ya raba musu kudade masu yawa a matsayin tallafi

- Sai dai ya bukaci wadanda su kayi alkawari zasu bayar da tallafinsu da su daure su kawo

Yau Talata ‘yan Kasuwar jihar Kano da Gobara ta shafa a shekarar da ta gabata zasu kai Azuminsu cikin farinci sakamakon tallafi rage radadi da Gwamnatin jihar tayi musu da ya kai Naira biliyan N1.3b.

Sanarwar bayar da tallafin dai ta fito ne yau daga wani jawabi da jami’in yada labarai na Ofishin Mataimakin Gwamnan jihar Alhaji Balarabe Abdullahi ya fitar.

Gwamnatin Kano ta gwangwaje ‘yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar da zunzurutun kudi har N1.3bn

Gwamnatin Kano ta gwangwaje ‘yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar da zunzurutun kudi har N1.3bn

Sanarwar ta bayyana cewa Mukaddashin Gwamnan jihar Farfesa Hafiz Abubakar ne ya kaddamar da bayar da tallafin kashi na biyu ga wadanda Gobarar ta shafa a yau.

Gwamnatin Kano ta gwangwaje ‘yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar da zunzurutun kudi har N1.3bn

Gwamnatin Kano ta gwangwaje ‘yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar da zunzurutun kudi har N1.3bn

KU KARANTA: An fara bawa jami'an 'Yan sanda 150 horo ta musamman kan yaki da ta'addanci

Mataimakin Gwamnan dai shi ne shugaban Kwamitin bayar da tallafin ga 'yan kasuwar, kuma ya shaida cewa ya zuwa yanzu Kwamitin ya bayar da cakin kudi ga Mutane 5, 671 da abin ya shafa.

Gwamnatin Kano ta gwangwaje ‘yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar da zunzurutun kudi har N1.3bn

Gwamnatin Kano ta gwangwaje ‘yan Kasuwar da Gobara ta yiwa barna a jihar da zunzurutun kudi har N1.3bn

Sannan ya bayyana cewa har yanzu akwai adadin N345 da wadanda su kayi alkawari ba su bayar ba, a saboda haka ne yayi kira gare su da su taimaka su cika alkawarin da suka dauka.

Farfeasan ya kuma ce wannan karon Mutane 191 suka amfana da rabon, kana daga karshe ya bayar da tabbacin raba kudin ga wadanda suka cancanta da zarar wadanda su kayi alkawarin sun bayar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel