Yanzu-Yanzu: Hukumar DSS ta maido wa Saraki masu tsaron sa da aka janye

Yanzu-Yanzu: Hukumar DSS ta maido wa Saraki masu tsaron sa da aka janye

- Hukumar tsaron farar hula DSS ta mayar wa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wasu daga cikin masu tsaronsa da aka janye

- Hukumar DSS din ta janye kashi biyu cikin uku na masu tsaron shugaban majalisar Bukola Saraki tun a ranar 2 ga watan Yuni

- A yanzu, babu tabbas ko an dawo wa Yakubu Dogar da Ike Ekweremadu masu tsaron nasu da aka janye

A yau Talata 5 ga watan Yuni ne Hukumar tsaro na kasa (SSS) ta mayar wa Shugaban Majalisar Bukola Saraki sauran masu tsaronsa da aka janye a kwanakin baya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa hukumar yan sandan sirrin ta janye kashi biyu cikin uku na masu tsaron Saraki da sauran shugabanin majalisar guda uku a ranar Asabar 2 ga watan Yuni.

Yanzu-Yanzu: Hukumar DSS ta maido wa Saraki masu tsaron sa da aka janye

Yanzu-Yanzu: Hukumar DSS ta maido wa Saraki masu tsaron sa da aka janye

Rahotanni sun ce an janye sama da jami'an tsaro 12 daga cikin tawagar Bukola Saraki kawai amma a yanzu wata majiya da ke kusa da shugbanan majalisar dattawan ya tabbatar da cewa an maido da guda biyar.

KU KARANTA: Talauci ya sanya na sayar da jariri na kan kudi N670,000 - Wata matashiya 'yar shekaru 17

A halin yanzu, babu cikaken bayani dangane ta mayar wa kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da mataimakin majalisar dattawa Ike Ekweremadu da mataimakin kakakin majalisar wakilai Yusuf Lasun na su masu tsaron.

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito muku cewa shugaban majalisa Bukola Saraki ya fara shirye-shiryen amsa gayyatar yan sanda bisa zargin da ake masa na daukan nauyin yan fashin da su kayi fashin banki a Offa na jihar Kwara.

Saraki ya sanar a jiya Litinin 4 ga watan Yuni ta shafin sadarwarsa na Twitter @bukolasaraki cewa ya aika mai tsaron sa ya tafi ya karbo wasikar gayyatan daga yan sanda saboda ya shirya yadda zai kare kansa daga zargin da ake masa na hannu cikin fashin Offa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel