Yara 152m ke Aikin 'Kwadago duk Shekara a fadin Duniya - ILO

Yara 152m ke Aikin 'Kwadago duk Shekara a fadin Duniya - ILO

Wani sabon rahoto da sanadin shafin jaridar The Nation ya bayyana cewa, akwai adadin kimanin yara miliyan 152 dake afkawa cikin kangi na aikin kwadago a kowace shekara a fadin duniya.

Shugaban cibiyar kwadago ta Duniya watau International Labour Organisation (ILO), Guy Ryder, shine ya bayyana hakan a yayin tunawa da ranar yaki da aikin kwadogo na yaran duniya.

Shugaban Cibiyar ILO; Guy Ryder

Shugaban Cibiyar ILO; Guy Ryder

Cikin taron karo na 107 da aka gudanar a Birnin Geneva dake kasar Switzerland, Mista Ryder ya bayyana cewa akwai kimanin yara wadanda suke a tsakanin shekaru 5 zuwa 17 dake afkawa cikin tarkon aikin kwadago a kowace shekara a fadin Duniya.

A sanadiyar haka shugaban ya kirayi shugabannin Duniya akan su tashi tsaye wurjanjan wajen shawo wannan matsala domin magance ta tun daga diddigin ta.

Yake cewa, hakan zai taimaka kwarai da aniyya wajen rage adadin yara dake afkawa cikin kangin aikin kwadago a fadin Duniya da yake janyo tabarbarewar rayuwar su tun kafin su san ciwon kawunan su.

KARANTA KUMA: Dalilai da suka sanya Sakataren Kwamitin Gangamin Jam'iyyar APC ya yi Murabus

Jagoran Cibiyar ya ci gaba da cewa, wannan adadi na yara masu aikin kwadago yana hauhawa ne musamman a sakamakon yadda mafi akasarin iyaye ke tilastawa 'ya'yen su aikin noma a gonakin su ba tare da wani biyan su lada ba na taro ko sisi.

A na sa bangaren, wani jagoran yakar aikin kwadagon yara, Kailash Satyarthi ya bayyana cewa akwai aiki ja a gaba wajen kawar da wannan kalubale a fadin Duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel