Yanzu - yanzu: ICPC ta bada belin Darakta Janar Munir Gwarzo

Yanzu - yanzu: ICPC ta bada belin Darakta Janar Munir Gwarzo

Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa (ICPC) ta kama tsohon darakta janar na kwamitin canje - canjen tsaro wato Securities and Exchange Commission (SEC) a turance, Munir Gwarzo da zargin almundahana da wasu kudade

Yanzu - yanzu: ICPC ta bada belin Darakta Janar Munir Gwarzo

Yanzu - yanzu: ICPC ta bada belin Darakta Janar Munir Gwarzo

Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa (ICPC) ta kama tsohon darakta janar na kwamitin canje - canjen tsaro wato Securities and Exchange Commission (SEC) a turance, Munir Gwarzo da zargin almundahana da wasu kudade.

DUBA WANNAN: Matsaloli guda 5 dake tattare da mulki a Najeriya - Gwamnan Bauchi

A laifukan da aka bayyana a gaban babbar kotun birnin tarayya, an kama shi da laifuffuka guda biyar a ciki harda na kwamishinan ma'aikatar Zakawani Garba wanda aka kama shi da laifin ya biya kansa kudade masu dumbin yawa, da suka hada da kimanin naira miliyan 104.8 da kuma naira miliyan 10.4 a lokacin da yake kan aiki.

A yanzu haka dai alkalin babbar kotun tarayyar Hussein Baba-Yusuf ya bada belin su akan kudi naira miliyan 25 kowannen su sannan kuma su gabatar da shaidu.

Alkalin ya bayyana cewar dole shiadun su zamanto wadanda suke aiki a gwamnatin tarayya kuma kada suyi kasa da matsayin mataimakin darakta.

Ku biyo mu zamu kawo muku yanda ta kaya a gaba...

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel