Kachikwu da Adeosun sunyi watsi da gayyatar da Saraki yayi musu

Kachikwu da Adeosun sunyi watsi da gayyatar da Saraki yayi musu

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya nuna bacin ransa akan watsi da gayyatar da yayiwa karamin ministan man fetur, Dr Ibe Kachikwu da ministan kudi, Kemi Adeosun sukayi

Kachikwu da Adeosun sunyi watsi da gayyatar da Saraki yayi musu

Kachikwu da Adeosun sunyi watsi da gayyatar da Saraki yayi musu

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya nuna bacin ransa akan watsi da gayyatar da yayiwa karamin ministan man fetur, Dr Ibe Kachikwu da ministan kudi, Kemi Adeosun sukayi.

Kwamitin hadin guiwa na masana'antar man fetur na majalisar wanda Sanata Kabir Marafa (APC), Zamfara) ke shugabanta, ya kira ministocin tataunawa akan abubuwa uku na masana'antar man fetur amma duk cikin su babu wanda ya halarci taron.

DUBA WANNAN: Buhari yaki saka hannu a kasafin kudin 2018 da majalisa ta gabatar mishi

Saraki yace rashin halartar ministocin sam bai yi dadi ba.

Marafa, bayan ya gama kiran sunayen wadanda suka halarci tataunawa,yace an gayyaci ministocin ne don su bada gudummawarsu a tattaunawar.

Bayan ministocin, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele da babban akawun kasar, Ahmed Idris, basu halarci tattaunawar ba.

Marafa yace, "Babu dadi ace zamu tataunawa muhimman abubuwa ba tare da mutanen nan ba. Ina fatan hakan baza ta kara faruwa ba."

"Mun kara musu lokacin gayyatar. Idan bamu ga wasu canje canje zuwa gobe ba, zamu sanar da shugaban kasa. Shine babban ministan man fetur kuma yana da ra'ayin abubuwan da zamu tattauna akai. Zamu basu zuwa gobe (yau kenan) " yace.

Akan abubuwan da zasu tattauna, Saraki yace sababbin tsarin da majalisar ta fitar zai kara habako tattalin arziki kuma zai kaimu ga tsari mafi kyau ta bangaren man fetur.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel