An hana Shittu da Aisha Alhassan shiga wajen taron kaddamar da shugabannin APC

An hana Shittu da Aisha Alhassan shiga wajen taron kaddamar da shugabannin APC

Rahotanni sun kawo cewa an hana ministocin gwamnati mai ci guda biyu, Aisha Alhassan na harkokin mata da Adebayo Shittu na sadarwa shiga wajen taron kaddamar shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa taron ya hargite a yayinda shugabannin da suka fito ke kokarin ganin hankula sun ja hankulan jama’a.

An tattaro cewa jami’an tsaro na ta kokarin ganin sun dakatar da sabanin da ya kaure tsakanin yan jam’iyyun da magoya bayansu.

A cewar NAN, duk da kokarin da jami’an tsaro na Alhassan da Shittu sukayi don ganin sun shigar da su ciki, basu samu damar shiga dakin taron ba.

An hana Shittu da Aisha Alhassan shiga wajen taron kaddamar da shugabannin APC

An hana Shittu da Aisha Alhassan shiga wajen taron kaddamar da shugabannin APC

An rahoto cewa lamarin ya haddasa takun saka daga magoya bayan gamayyar da aka hana shiga dakin inda har said a ya kai jami’an tsaron sun harba barkonon tsohuwa ga masu zanga-zangar.

KU KARANTA KUMA: Kalli mummunan yanayin da wani asibitin Arewa ke ciki (hotuna, bidiyo)

Aisha Alhassan a nata bangaren tace abun bai dame tab a domin irin hakan ba sabon abu bane a siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel