Yanzu Yanzu: Buhari, Osinbajo sun gana da shugabannin tsaro

Yanzu Yanzu: Buhari, Osinbajo sun gana da shugabannin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo sunyi ganawa daban daban da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 4 ga watan Yuni.

Da farko shugaban kasar ne ya fara ganawa da shugabannin tsaro da shugabannin hukumomin tsaro inda daga bisani mataimakin shugaban kasar ya gana da sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris, darakta janar na hukumar DSS, Lawal Daura da minstan shari’a Abubakar Malami.

Anyi dukkanin ganawar ne a cikin sirri.

Koda dai Sufeto Janar na yan sanda ya ki bayyana manema labarai cikakken bayani akan ganawar tasu wanda ya kwashe tsawon sa’o’i biyu ana ganin cewa yana da nasaba da lamarin dake gudana a yanzu tsakanin Bukola Saraki da hukumar yan sanda.

Buhari, Osinbajo sun gana da shugabannin tsaro

Buhari, Osinbajo sun gana da shugabannin tsaro

A ranar Lahadi ne hukumar yan sanda ya gayyaci shugaban majalisar dattawa domin ya amsa wasu tambayoyi bayan an kama mutanen da suka yi fashin Offa jihar Kwara inda suka ambaci sunansa cikin masu daukar nauyinsu.

KU KAANTA KUMA: An hana Shittu da Aisha Alhassan shiga wajen taron kaddamar da shugabannin APC

Masu laifin sunyi ikirarin cewa su Karen siyasan shugaban majalisar dattawa da gwamnan jihar Kwara, Abdulfata Ahmed ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel