Talauci ya sanya na sayar da jariri na kan kudi N670,000 - Wata matashiya 'yar shekaru 17

Talauci ya sanya na sayar da jariri na kan kudi N670,000 - Wata matashiya 'yar shekaru 17

- Yan sanda sun kama wata matashiya mai shekaru 17, Gift Daniel, cikin gungun wasu masa safarar mutane a jihar Abia

- An gano cewa Daniel ta siyar da jaririnta bayan kwanaki biyu da haihuwa a kan N670,000

- Ta shaidawa manema labarai cewa ta siyar da jaririn ta ne saboda talauci da suke fama dashi a gidansu

Rundunar Yan sandan jihar Abia ta damke wasu mutane da ke kungiyar masu safarar da yara wanda suka kware wajen sayar da jarirai cikinsu har da wata matashiya yar shekara 17, Gift Daniel wanda ta sayar da jaririnta bayan kwanaki biyu da haihuwarsa kan N670,000.

Kwamishinan Yan sandan jihar, Anthony Ogbizi ne ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin 6 ga watan Yuni a garin Umuahia yayinda ya ke bayani kan ayyukan rundunar.

'Yan sanda sun damke wata matashiya da ta siyar da jaririnta a kan kudi N670,000

'Yan sanda sun damke wata matashiya da ta siyar da jaririnta a kan kudi N670,000

Ogbizi ya kara da cewa rundunar ta kuma kama wasu mutane 22 da ake zargi da aikata wasu miyagun ayyuka a sassa daban-daban na jihar kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

KU KARANTA: An fara bawa jami'an 'Yan sanda 150 horo ta musamman kan yaki da ta'addanci

A hirar da tayi da manema labarai, matashiyar Daniel ta shaida musu cewa talauci ne ya sanya ta siyar da jaririn nata.

Ta kuma shaidawa manema labaran cewa mahaifiyarta ce ta fara sayar da 'dan da ta haifa da farko hakan yasa tayi niyyar sayar da wannan da kanta.

Ta ce: "Mahaifiyata ta kore ni daga gidan mu bayan na samu ciki karo na biyu saboda ba za ta iya kulawa da ni ba, hakan yasa na fara neman wanda zai taimaka min."

Daniel ta ce wata mata mai suna Mgozi Nwaiwu ta biya ta N50,000 sannan da biya unguwar zoman da ke taimaka mata, Kate Charles, N30,000.

Nwaiwu ta tabbatar wa yan sanda batun cinikin siyan jaririn inda ta ce tayi hakan ne saboda ta taimakawa yarinyar saboda halin da ta ke ciki.

Har ila yau, yan sandan sun kuma kama wata Blessing Chukwu mai shekaru 22 wanda aka samu ta sayar da jaririyarta ga wata Chinasa Okpara mai shekaru 40. Sauran wanda aka samu da hannu cikin cinikin sun hada da mijin matan, Puphemia Omende da mijinta Kelechi wanda likita ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel