An garkame wadanda ake zargi da laifin kashe Fastoci a Jihar Benuwe a gidan yari

An garkame wadanda ake zargi da laifin kashe Fastoci a Jihar Benuwe a gidan yari

Wani Alkalin Kotun Majistare da ke Garin Benuwe mai Isaac Ajim ta aika tsohon Shugaban Jami’in tsaron sa-kai daga Makiyaya na Gwamnatin Jihar Alhaji Tashaku Aliyu a game da kisan wasu Malaman addini a wani Kauye kwanakin baya.

Ana zargin Tashaku Aliyu da laifin kashe wasu Fastoci 2 da kuma wasu mutane 17 a wani babban asibitin Katolika “St. Ignatius Catholic” da ke Kauyen Ukpor, Ayar a Garin Mbalom. Wannan Gari dai na cikin Karamar Hukumar Gwer.

An garkame wadanda ake zargi da laifin tada fitina a Jihar Benuwe a gidan yari

Alkali ya sa a aika Aliyu Tashaku da wasu zuwa gidan yari

Bayan Tashaku Aliyu, wadanda aka aika kurkuku sun hada da Husseini Manga, Ngyohov Shin, David Akenawe, Agada Tsesaa da Tarza Orvanya. Duk wadannan mutane su na cikin Jami’an tsaron nan na “Livestock Guards” na Jihar.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya bayyana matsalolin mulki a Najeriya

Kwanaki ne Gwamnatin Jihar Benuwe ta kirkiro “Livestock Guards” inda aka kuma ba su makamai. Ana zargin wadannan Jami’an tsaro sun rika taimakawa Makiyaya wajen kashe manoma a cikin Jihar a gaban Alkali mai shari’a.

Kwanakin baya ne Jami’an SARS, DSS, da Sojojin Najeriya su ka damke Tashaku Aliyu aka kuma wuce da shi Abuja domin bincike. Yanzu dai an maka su a Kurkukun Garin Makurdi har sai lokacin da aka tike shari’a a watan Gobe.

Ana dai zargin cewa Aliyu Tashaku tsohon ‘Dan kungiyar Boko Haram ne a Arewa maso gabashin kasar. Daga baya ne Gwamna Samuel Ortom ya ba shi aiki a Gwamnati domin kare manoman Jihar bayan kafa wata dokar haramta kiwo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel