Kawunan Malaman Addini sun rabu kan Miliyan N260 da kuma magudin fitar da shugaba

Kawunan Malaman Addini sun rabu kan Miliyan N260 da kuma magudin fitar da shugaba

-Rigirmar cikin gida ta turnuke kungiyar mabiya darikar Anglican a jihar Legas

- Har ta kai ga garzayawa zuwa Kotu domin raba gardama

- Yanzu haka Alkalin dake shari'ar ma ta sauka har an nada sabon Alkali

Wasu fusatattun tsagin shuwagabannin kungiyar Kiristoci mabiya darikar Anglica sun shigar da kara gaban wata babban Kotun Tarayya domin a biya musu bukatunsu uku.

Daga cikin bukatar masu karar akwai dakatar da wadanda ake karar daga duk wani yunkuri na cigaba da aniyarsu ta tsige sabon shugaban Halarar Humphrey Olumakaiye har sai Kotun ta yanke hukunci.

Tsakanin dan Adam da Kudi: Kawunan Malaman Addini sun rabu kan Miliyan N260 da kuma magudin fitar da shugaba

Tsakanin dan Adam da Kudi: Kawunan Malaman Addini sun rabu kan Miliyan N260 da kuma magudin fitar da shugaba

Masu shigar da karar sune; Fola Osibo, Modupe Alakija, Oluyomi Finnih, Femi Adeniyi-William, Layi Ajayi-Bembe, Laide Sasegbon, Modupe Sagoe, Ade Abisogun, Bukola Meadows, da kuma Molara Otuyelu, sun bayyana kansu a matsayin dakarun sanya ido kan shige da ficen kudin Majami’ar kuma masu kishin cigaban Halarar reshen jihar ta Legas.

Masu karar dai suna ikirarin cewa an tafka magudi da kuma kaucewa ka’ida yayin fitar da shugaban Halarar.

Sannan kuma suna bukatar Kotun ta umarci guda daga cikin dan Kwamitin amintattaun kuma shugaban Halarar na yanzu Bishop Adebola Ademowo da ya dawo da wasu makudan kudade da suka kai Miliyan N260m da ya karba ya karkatar da su domin biyan bukatar kansa.

KU KARANTA: An kai Saraki da Mataimakinsa kara Kotu a dalilin IGP Ibrahim Idrsi

Yayin da su kuma wadanda ake karar suka kunshi Kwamitin amintattu na Majami’ar da kuma Rev Nicholas Okoh da Adebola Ademowo da Humphrey Olumakaiye da kuma Michael Fape.

Tun farko dai karar mai shari’a Chuka Obiozor ne ya fara sauraronta kafin daga bisani a mikawa Ms Olatoregun domin cigaba da shari’ar.

Amma sai dai canza alkalin ya sanya wadanda ake karar rubutawa sabuwar alkalin wasika suna shawartarta da ta janye tare da bawa wani alkalin ya cigaba da sauraren shari'ar, kasancewarta mabiyyiyar Halarar Majami'ar sau da kafa.

An dai rawaito cewa a zaman Kotun na karshe wanda aka gudanar a bayyanar jama'a ta mikawa wani sabon Alkali mai suna Rilwan Aikawa domin ya cigaba da jagorantar shari’ar.

Yanzu haka dai an dage sauraren karar zuwa ranar 21 ga watan Yuli domin cigaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel