Gurfanar da gwamnonin PDP ba bita da kulli bane - Magu

Gurfanar da gwamnonin PDP ba bita da kulli bane - Magu

Mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, ya ce gurfanar da wasu tsaffin gwamnonin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ba siyasa bane kuma ba bita da kulli bane.

Magu ya bayyana hakan ne bayan kaddamar da taron ganawa akan yaki da rashawa da cibiyar cigaban Afirka, New Partnership for Africa’s Development (NEPAD Nigeria) ta shirya.

Yayinda yake amsa tambayoyi kan maganar cewa me yasa tsaffin gwamnonin jam’iyyar PDP irinsu Ibrahim Shekarau da Ramalan Yero aka dukufar kan kudin zaben 2015, Magu yace “Babu wanda yace mun damke wasu ba tare da hujjarmu ba.

Gurfanar da gwamnonin PDP ba bita da kulli bane - Magu

Gurfanar da gwamnonin PDP ba bita da kulli bane - Magu

“Muna bincike ne bisa ga hujjoji kuma babu wanda ya musanta hakan. Bamu taba kama mutum bisa dalilai maras karfi ba. Kamar al’ada, muna gudanar da bincike mai zurfi kuma mu tafi kotu bisa ga hujja”

KU KARANTA: Ku Godewa Allah da ya baku Buhari a matsayin shugaban kasa – cewar wani babban Malami

Magu yace akwai bukatan kasashen Afrika suyi amfani da kwarewan wasu domin tabbatarwa duniya cewa dole ayi hisabin dukiyan da aka sace.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel