Gwamnatin tarayya ta haramta shan Shisha

Gwamnatin tarayya ta haramta shan Shisha

Gwamnatin tarayyar Najeeriya ta haramta shan sigari mai sinadari wanda aka fi sani da Shisha a bainar jama’a kuma ta umurci dukkan hukumomin tsaro da su damke duk wanda aka gani yana shan wannan abu a bainar jama’a.

Ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewole, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a birnin tarayya Abuja wajen taron da aka shirya domin murnan zagayowan ranan ganyen sigari na duniya.

Minista ya laburta cewa Najeriya na yin asaran kudi $800 million a kowani shekara kan cutar bugun jinni, cutar zuciya da ciwon siga sanadiyar yawan shan ganyen sigari a kasar.

Gwamnatin tarayya ta haramta shan Shisha

Gwamnatin tarayya ta haramta shan Shisha

Ya kara da cewa hujjan masana lissafi ya nuna cewa Najeriya na asarar makudan kudi wajen warkar da ciwon da sigari ke janyowa sama da ribar da ake samu kan sigari.

Saboda wannan abun takaici da kuma mutuwan mutane a kowani shekara sanadiyar wannan abu, za’a samar da sabuwar doka domin kawar da wannan abu.

Yace: “Dokar zai kunshi ilmantar da tilasta hana shan taba da kuma haramtar da sayarwa yan kasa da shekaru 18. Sannan kuma haramta tallar taba, haramta sha a bainar jama’a da kuma haramta sayarwa kasa da kwali 20.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel