APC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har illa ma sha Allah - Mama Taraba

APC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har illa ma sha Allah - Mama Taraba

A daidai lokacin da guguwar zaben 2019 ke kara gabatowa, Ministar dake kula da harkokin mata, kuma yar fadar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Aisha Alhassan wacce aka fi sani da Mama Taraba tayi tsokaci akan zabe mai zuwa.

Ministar ta jaddada cewa ko shakka bata yi akan cewa jam’iyyar APC mai mulki ce zata ci gaba da mulkar Najeriya har illa ma sha Allah.

A cewarta rikicin da am’iyyar ke fama da ita a halin da ake ciki ba wani sabon abu bane a harkar siyasa.

Ta kara da cewa daga lokacin da jam’iyyar ta gudanar da zaben shugabanninta na kasa toh babu shakka zata iya tunkarar kowace jam’iyyar siyasa a 2019.

APC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har illa ma sha Allah - Mama Taraba

APC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har illa ma sha Allah - Mama Taraba

A halin da ake ciki, Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.

KU KARANTA KUMA: Za mu dauki gandurobobi aiki saboda magance matsalolin gidan yari – Dambazau

Ta jaddada cewa kowa ya san cewa ita ce ta lashe zaben gwamnan jihar ta Taraba ba don zagon kasa da aka shirya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel