An kai Saraki da Mataimakinsa kara Kotu a dalilin IGP Ibrahim Idrsi

An kai Saraki da Mataimakinsa kara Kotu a dalilin IGP Ibrahim Idrsi

- Satoka sakatsin dake tsakanin Shugaban 'Yan sanda na kasa da Shugaban Majalisar Dattijai ya ya dauki sabon salo

- Inda wani Lauya ya kai Majalisar da Shugabanta da Mataimakinsa kara Kotu a Abuja

-An dai fara zaman Doya Manja ne tsakanin IGP da Saraki ne tun bayan gayyatar shi da su kayi yaki zuwa

Wani Lauya ya shigar da kara gaban wata babbar Kotu a Abuja yana kalubalantar Majalisar Dattijai da shugabanta Abubakar Bukola Saraki da Mataimakinsa Ike Ekeremadu bisa ayyana babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa (IGP) Ibrahim Idris a matsayin wanda bai cancanta da rike wani mukami a ciki ko wajen kasar nan ba da kuma bayyana shi a matsayin Makiyin Dimukuradiyya.

An kai Saraki da Mataimakinsa kara Kotu a dalilin IGP Ibrahim Idrsi

An kai Saraki da Mataimakinsa kara Kotu a dalilin IGP Ibrahim Idrsi

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa daga cikin bukatun da Lauyan ya shigar sun hada da; amincewa cewa shugaban Majalisar Dattijan Abubakar Bukola Saraki da Mataimakinsa Ike Ekeremadu ba su da wani hurumi na ayyana shi a matsayin makiyin Dimukuradiyya, sannan kuma Lauyan yana son Kotun ta bayyana kiranyen da Majalisar takewa shugaban ‘Yan sandan kan batun Sanata Dino Melaye a matsayin rashin bin ka’idar aiki da kuma katsalandan ga Rundunar ‘Yan sandan.

KU KARANTA: IGP Idris ya samu yardan Buhari wajen kama Saraki akan kisan Kwara

A kwanan baya dai mun kawo mu rahotan yadda Majalisar ta ayyana IGP Ibrahim Idris a matsayin makiyin Dimukuradiyya bayan da ya bijirewa gayyatar bayyana a gaban Majalisar domin amsa tambayoyi har sau uku.

Hakan ce ta sanya shugaban Majalisar Bukola Saraki bayan wani zama da ta yi ranar 9 ga watan Mayu ya bayyana cewa Ibrahim Idris din bai cancanta da rike kowanne Ofishi na Gwamnati a gida Najeriya ko a kasar waje ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel