Zaben 2019: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

Zaben 2019: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

Gwamnan jihar Ekiti dake zaman daya daga cikin manyan 'yan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya watau Gwamna Ayodele Fayose ya shawarci shugaban da ya janye kudurin sa na yin tazarce ya baiwa matasa dama masu jini a jika.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a dandalin sadarwar zamani na tuwita inda ya ce shekarun shugaban kasar sun wuce a ce yana mulkar 'yan Najeriya yanzu.

Zaben 2019: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

Zaben 2019: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

KU KARANTA: Cigaba da tsare Zakzaky rashin adalci ne - Buba Galadima

Legit.ng dai ta samu cewa a jiya ne shugaban kasar ya sanya sabuwar dokar rage shekarun tsayawa takara a Najeriya hannu.

A wani labarin kuma, Kamar yadda muke samun labari daga majiyoyin mu, alkalin wani babbar kotu a jihar Oyo Mai shari'a ML Owolabi ya ranar Litinin din da ta gaba ya yi mursisi ya hana bukatar da tsohon gwamnan jihar Otunba Adebayo Christopher Alao-Akala ya shigar a gabanta bisa ga shari'ar da yakeyi da hukumar EFCC.

Shi dai tsohon gwamnan, kamar yadda muka samu, ya shigar da wata kara ce a gaban kotun koli ta kasa yana kalubalantar shari'ar da ake yi masa kuma yanzu haka yana jiran tsammanin hukunci daga gare su.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel