Sauye-sauye: Kasar Saudiyya ta fara baiwa mata lasisin yin tuki

Sauye-sauye: Kasar Saudiyya ta fara baiwa mata lasisin yin tuki

- Kasar Saudiyya ta fara baiwa mata lasisin yin tuki

- Mata za su fara yin tuki a kasar ta daga ranar 24 ga watan nan na Yuni

- Lamarin dai ya dauki hankulan al'umma da dama musamman ma musulmi

A wani mataki na yunkurin kawo sauye-sauye a kasar ta, karon farko mun samu cewa kasar Saudiyya a hukumance ta fara baiwa mata lasisin yin tuki a kasar ta daga ranar 24 ga watan nan na Yuni da muke ciki mai zuwa.

Sauye-sauye: Kasar Saudiyya ta fara baiwa mata lasisin yin tuki

Sauye-sauye: Kasar Saudiyya ta fara baiwa mata lasisin yin tuki

KU KARANTA: Shekaru 4 sun yi mana kadan - Osinbajo

Kamar yadda muka samu, mahukunta a kasar sun wasu mata ne a matsayin matakin farko domin fara koya masu yadda za su yi tukin tare kuma da fara basu lasisin yin hakan.

Legit.ng ta samu cewa lamarin dai ya dauki hankulan al'umma da dama musamman ma musulmi a dukkan fadin duniya biyo bayan wani faifan bidiyo daya bayyana a kafafen sada zumunta kunshe da yanda ake dankawa wata mata lasisin fara tukin nata.

Kafrin yanzu dai kasar Saudiyya na zaman kasa daya tilo a Duniya dake da dokar hana mata tuki.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel