Da sake: Jawabin Buhari na makon jiya na kunshe da nakasa – Farouk Kperogi

Da sake: Jawabin Buhari na makon jiya na kunshe da nakasa – Farouk Kperogi

- Manyan masana a harshen Turanci sun fara duba jawabin Shugaba Buhari

- Dr. Kperogi da ke Amurka yace akwai tawaya a wani jawabin Shugaban kasa

- Kwanaki Shugaban Kasar yayi wani jawabi a Ranar bikin Damukaradiyya

A karshen makon da ya wuce ne wani babban Malamin Turanci kuma kusan Farfesa a fannin, Farouk Kperogi yayi magana game da Turancin Shugaban Kasa Buhari inda yace akwai wasu gyare-gyare a jawabin da Shugaban kasar yayi a makon jiya.

Da sake: Jawabin Buhari na makon jiya na kunshe da nakasa – Farouk Kperogi

Farouk Kperogi yace akwai tawaya a Jawabin Shugaban Kasa

Idan ba ku manta ba Shugaba Buhari yayi wa ‘Yan Najeriya jawabi a Ranar Damukaradiyya wanda babban Shehin Malamin na wata Jami’a a Kasar Amurka yace za a ga cewa akwai inda Shugaba Buhari yayi wasu kuskure a cikin jawabin na sa.

KU KARANTA:

A lokacin Shugaban Kasa Jonathan, Farfesan ya rika duba Turancin sa duk lokacin da yayi magana don haka wasu su ka nemi wannan karo ma dai ya bibiyi Turancin Shugaba Buhari ko da dai shi bai yi zurfi a karatun Boko na zamani ba kamar Jonathan.

Farouk Kperogi yace tun a tashin farko Shugaba Buhari ya fara kuskure a jawabin na sa na wancan makon, sannan kuma yace akwai inda aka sabawa ka’idar Nahawu lokacin da Shugaban Kasar yake magana kan masu garkuwa da mutane a Najeriya.

Babban Malamin Jami’ar dai yace ya kamata masu lura da jawabin Shugaban su rika tantance Turancin sa saboda Duniya na koyi ne da su. Kwanaki ma dai wani tsohon Malamin Makaranta a Amurka yayi kaca-kaca da wata wasika ta Donald Trump.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel