Buhari yaki saka hannu a kasafin kudin 2018 da majalisa ta gabatar mishi

Buhari yaki saka hannu a kasafin kudin 2018 da majalisa ta gabatar mishi

Gwamnatin tarayya tace shugaban kasa Muhammadu Buhari yana sake duba kudurin kasafin kudin 2018 da majalisar dokoki ta gabatar mishi a kwanakin baya

Buhari yaki saka hannu a kasafin kudin 2018 da majalisa ta gabatar mishi

Buhari yaki saka hannu a kasafin kudin 2018 da majalisa ta gabatar mishi

Gwamnatin tarayya tace shugaban kasa Muhammadu Buhari yana sake duba kudurin kasafin kudin 2018 da majalisar dokoki ta gabatar mishi a kwanakin baya. Ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Udoma Udoma, shine ya sanar da hakan, jim kadan bayan ganawar su da shugaban kasa a jiya Litinin.

DUBA WANNAN: Ana yiwa Ramos barazanar kisa

Majalisar dokoki ta gabatar da kudurin kasafin kudin 2018 a watan daya gabata, a shekarar data gabata an gabatarwa da shugaban kasar kasafin kimanin naira tiriliyan 8.612, sabanin wannan suka gabatar da kimanin naira tiriliyan 9.120.

A ranar juma'ar data gabata ne aka gabatarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kasafin kudin.

Da aka tambayeshi menene dalilin da yasa shugaban kasar bai rattaba hannu akan kudurin ba, sai yace, "A halin yanzu shugaban kasar yana sake duba kudurin kasafin kudin ne da aka gabatar masa, kuma kamar yanda kuka sani har yanzu muna da sauran kwanaki 30 kafin lokaci ya kure.

"Shugaban kasar yana iya bakin kokarin sa wurin ganin ba'a samu matsala a kudurin da aka gabatar masa ba, amma na tabbatar muku da cewar da ya gama dubawa zai saka hannu. Wannan shine abinda zan iya ce muku a yanzu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel