2019: Abunda Arewa zata duba wajen marawa yan takarar shugaban kasa baya - Yakasai

2019: Abunda Arewa zata duba wajen marawa yan takarar shugaban kasa baya - Yakasai

Shugaban kungiyar dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana dattawan Arewa basu tsayar da ko wani dan takara ba tukuna a tsakanin jam’iyyun APC da PDP a 2019.

Yakasai ya bayyana cewa tsayarwarsu zai kasance akan manufofin yan takara ba wai sanayar halayensu ba,” jaridar Punch ta ruwaito.

Yakasai ya bayyana cewa a baya Yan Najeriya sunyi kuskure, daga tsohon shugaban kasa Olusegun zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen zabar hallaya ba wai ingancin shirye-shiryen da yan takarar suka tanadar ba.

2019: Abunda Arewa zata duba wajen marawa yan takarar shugaban kasa baya - Yakasai

2019: Abunda Arewa zata duba wajen marawa yan takarar shugaban kasa baya - Yakasai

Ya bayyana cewa matasan arewa karkashin kungiyar Coalition of Northern Youths, na da damar da zasu kaddamar ko janye goyon bayansu daga shugaba Buhari ko tsohon mataimakin shugab an kasa, Atiku Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sabuwar PDP ta janye daga tattaunawa da APC

Yakasai yace a matsayin dattijo mai shekaru 93, ba zai sanya baki a lamuran matasa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel