Dambazau ya kai ziyara gidan yarin da 'yan bindiga suka fasa

Dambazau ya kai ziyara gidan yarin da 'yan bindiga suka fasa

Ministan cikin gida, Alhaji Abdulrahman Dambazau, ya ziyarci gidan yarin garin Minna babban birnin jihar Neja, wanda wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a tabbatar da su waye ba suka fasa a jiya Lahadi

Dambazau ya kai ziyara gidan yarin da 'yan bindiga suka fasa

Dambazau ya kai ziyara gidan yarin da 'yan bindiga suka fasa

Ministan cikin gida, Alhaji Abdulrahman Dambazau, ya ziyarci gidan yarin garin Minna babban birnin jihar Neja, wanda wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a tabbatar da su waye ba suka fasa a jiya Lahadi. Ziyarar ministan ta biyo bayan harin da 'yan bindigar suka kai a yankin Tunga dake birnin Minna.

DUBA WANNAN: Kowacce hukuma a Najeriya ta bayyana kasafin kudin ta amma banda majalisar dokoki

Rahoto ya tabbata cewar mutane biyu sun rasa rayukan su, inda aka tabbatar da cewa daya dan acaba ne, dayan kuma ma'aikacin gidan yarin ne.

A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin a gidan talabijin din Channels, mai magana da yawun ma'aikatan gidan yari na jihar Neja, Rabiu Shu'aibu, ya ce "Lamarin ya faru ne a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari gidan yarin, sunyi bata kashi da masu gadin gidan yarin, inda har aka samu asarar rayukan mutane biyu, ma'aikacin gidan yarin da kuma wani dan acaba.

"Har ya zuwa yanzu ba'a tabbatar da fursunoni nawa bane suka gudu gidan yarin, duk da dai cewar an samu nasarar kama da yawa daga cikin su.

"A halin yanzu dai hukumar gidan yari ta jihar Neja tana daukan sunayen wadanda suka rage a gidan yarin, inda hakan shine zai bada tabbacin mutane nawa ne suka gudu."

A karshe hukumar gidan yarin ta sanar da jama'a unguwar dasu cigaba da gabatar da harkokin su kamar yanda suka saba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel