‘Yan bindiga sun fara karbar haraji wurin duk mai son noma gonar sa a jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun fara karbar haraji wurin duk mai son noma gonar sa a jihar Zamfara

Al’amuran tsaro a Zamfara sun dauki sabon salo bayan da ‘yan bindigar da suka addabi mutanen jihar da kasha-kashe suka kakabawa manoma biyan haraji kafin su noma gonakin su.

Mutanen jihar ta Zamfara na cigaba da zama cikin zulumi da tashin hankali bisa halin da ‘yan bindiga, da suka hada da barayin shanu da ‘yan fashi suka jefa rayuwar mutane a ciki.

A wata hira da gidan Radiyon Faransa tayi da Bashir Ibrahim Idris, wani mazaunin jihar ta Zamfara, ya bayyana cewar matsalar tsaro a Zamfara na kara tabarbarewa duk da kokarin da gwamnati ke yin a shawo kan al’amarin.

‘Yan bindiga sun fara karbar haraji wurin duk mai son noma gonar sa a jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari

Ko a yayin ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Amurka, ya shaidawa sashen Hausa na Radiyon Amurka cewar, an kasha mutane a jihar Zamfara fiye da wadanda aka kashe a jihohin Benuwe da Taraba dake fama da rikicin makiyaya da manoma.

DUBA WANNAN: An yiwa Kanu Fashi a filin jirgin saman kasar Rasha, an sace masa miliyoyi

Batun biyan ‘yan bindiga haraji kafin mutum ya noma gonar say a saka mazauna kauyuka cikin fargaba da tashin hankali ganin cewar mazauna kauyukan sun dogara ne kacokan a kan nomad a kiwo.

Bamu samu jin ta bakin hukumomin tsaro da na jihar Zamfara a kan wannan batu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel