Yanzu Yanzu: Saraki da Ýan sanda: Osinbajo na cikin ganawa mai muhimmanci da IGP Idris, SSS-DG Daura, AGF Malami

Yanzu Yanzu: Saraki da Ýan sanda: Osinbajo na cikin ganawa mai muhimmanci da IGP Idris, SSS-DG Daura, AGF Malami

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na ganawa mai muhimmanci tare da manyan jami’an gwamnati a yau Litinin, 4 ga watan Yuni.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa wadanda ake ganawar da su sun hada da sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris, darakta janar na SSS Lawal Daura, da kuma babban alkalin alkalai na tarayya Abubakar Malami.

An tattaro cewa ofishin mataimakin shugaban kasar tace babban dalilin ganawar akan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne.

Yanzu Yanzu: Saraki da Ýan sanda: Osinbajo na cikin ganawa mai muhimmanci da IGP Idris, SSS-DG Daura, AGF Malami

Yanzu Yanzu: Saraki da Ýan sanda: Osinbajo na cikin ganawa mai muhimmanci da IGP Idris, SSS-DG Daura, AGF Malami

Rundunar yan sanda ta aika sammaci ga Saraki a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuni bayan an zarge shi da daukar nauyin wasu yan fashi da makami biyar.

KU KARANTA KUMA: Hotunan kyawawan yaran shugabannin kasashen Afrika 10

Idan baaku manta ba an bayyana cewa a ranar Juma’a 1 ga watan Yuni, Idris ya gana da shugaba Buhari domin neman goyon bayansa wajen kama Saraki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel