Lauretta ta bayyana Buhari, Obasanjo da IBB a matsayin nagari, mugu da mummuna

Lauretta ta bayyana Buhari, Obasanjo da IBB a matsayin nagari, mugu da mummuna

A ranar Litinin, 4 ga watan Yuni hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie ta wallafa wani hoto na shugaban kasa Muhammadu Buhari, Olusegun Obasanjo da kuma Ibrahim Badamasi Babangida dauke da rubutu ‘Nagari, mugu da mummuna’, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Onochie wacce ta wallafa hoton a shafinta na Twitter ta tambayi jama’a ko suna da kwafin wasan Nagari, Mugu da Mummuna wato ‘The Good, Bad and Ugly’ sannan kuma tayi amfani da hoton su wajen bayanin wasan.

Zuwa yanzu dai hadimar shugaban kasar bat a bayar da wani dalili na wannan rubutu wanda ya janyo cece-kuce ba.

Sai dai wasu makaranta sun bayyana cewa rubutun da hoton na da nasaba da nasarorin da shugabannin lokacin gwamnatinsu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki da Ýan sanda: Osinbajo na cikin ganawa mai muhimmanci da IGP Idris, SSS-DG Daura, AGF Malami

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Obasanjo, tsohon shugabakasar Najeriya ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya sake takara a matsayin shugaban kasa a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel