Wani Matashi ya yiwa tsohuwar Kakarsa mai shekaru 80 lugudan Naushi

Wani Matashi ya yiwa tsohuwar Kakarsa mai shekaru 80 lugudan Naushi

- Gaggawa ta debi wani Matashi yayi katobara

- Matashin ya lallasa Kakarsa ne mai shekaru da yawa kawai don ta yi masa fada

- Amma sai dai da ake je Kotu ya ce shi bai san zancen ba

Wani saurayi mai shekaru 25 ya gurfana gaban Kotin Majistire dake zamanta a Yaba ta jihar Legas bisa zarginsa da zagewa ya lakadawa Kakarsa tsohuwa tukuf mai shekaru 80 duka.

Dan sanda mai gabatar da kara Sajan Modupe Olaluwoye ya shaidawa Kotun cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Mayu da misalin karfe 4:20pm na yamma a unguwar Bariga dake jihar ta Legas.

Wani Matashi ya yiwa tsohuwar Kakarsa mai shekaru 80 lugudan Naushi

Wani Matashi ya yiwa tsohuwar Kakarsa mai shekaru 80 lugudan Naushi

Wanda ake zargin dai ya nannaushi tsohuwar Kakar tasa ne mai suna Aina Giwa yayin da suke sa’insa da ita saboda tana yi masa fada da ya daina rigima da makwabta, shi kuma cikin fushi ya kai mata naushin da ya same ta a gadon bayanta.

KU KARANTA: Ku Godewa Allah da ya baku Buhari a matsayin shugaban kasa – cewar wani babban Malami

“Yanzu haka dai Matashin ya jiwa tsohuwar rauni sosai kuma ba don Mutanen dake kusa sun kai mata dauki ba da illar da zai mata na da yawa”.

Amma sai dai ga mamakin kowa shi ne yadda bayan karanto masa laifin da ake zarginsa da shi, ya ce shi bai akata komai ba.

Daga karshe sai mai shari’a Mrs O.J. Oghere ya bayar da belinsa kan kudi Naira 20,000 tare da kawo wanda zai tsaya masa.

Sannan ta dage zaman Kotun zuwa ranar 18 ga watan Yuli domin cigaba da sauraren shari’ar, kamar yadda NAN ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel