Majalisar dokoki ta boye nata kasafin kudin inda ta ki bayyanawa

Majalisar dokoki ta boye nata kasafin kudin inda ta ki bayyanawa

Bayan kari akan kudaden kashewarsu daga naira biliyan 125 zuwa naira biliyan 139.5, majalisar dokokin kasar ta barwa kanta sanin kasafin kudinta na 2018, jaridar Daily Trust ta rahoto.

A ranar 16 ga watan Mayu, lokacin da majalisar dokokin kasar ta gabatar da kasafin kudin kasar, kasafinta ya zo ne a layi guda ba tare da cikakken bayani ba.

Rahoto ya bayyana cewa bayan kwanaki 18 da gabatar da kasafin kudin 2018, majalisar dokoki ta ki bayyana cikakken kasafinta, ba kamar shekarar bara da aka saki bayanin ranar da aka gabatar da kasafin kudi.

Majalisar dokoki sun boye nasu kasafin kudin sun ki bayyanawa

Majalisar dokoki sun boye nasu kasafin kudin sun ki bayyanawa

Anyi kokarin tab akin kakakin majalisar dattawa, Aliyu Sabi Abdullahi (APC, Niger) sai dai yaki amsa kiran waya balle kuma sakon text da aka tura masa.

KU KARANTA KUMA: Yan biyun da ke rayuwa a hade sun mutu suna da shekaru 21 a duniya

Kakakingida, Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa) yace baa jimawa ba za’a saki cikakken bayani a lokacin da aka tuntube shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel