Kowacce hukuma a Najeriya ta bayyana kasafin kudin ta amma banda majalisar dokoki

Kowacce hukuma a Najeriya ta bayyana kasafin kudin ta amma banda majalisar dokoki

Bayan gwamnati ta kara musu kudin kashewar su daga naira biliyan 125 zuwa naira biliyan 139.5, majalisar dokokin kasar nan ta boye bayanin kasafin kudin ta na wannan shekarar, inda taki gabatar dashi kamar yanda kowacce hukuma tayi a kasar nan

Kowacce hukuma a Najeriya ta bayyana kasafin kudin ta amma banda majalisar dokoki

Kowacce hukuma a Najeriya ta bayyana kasafin kudin ta amma banda majalisar dokoki

Bayan gwamnati ta kara musu kudin kashewar su daga naira biliyan 125 zuwa naira biliyan 139.5, majalisar dokokin kasar nan ta boye bayanin kasafin kudin ta na wannan shekarar, inda taki gabatar dashi kamar yanda kowacce hukuma tayi a kasar nan.

A ranar 16 ga watan Mayu, majalisar dokoki ta yarda da tsarin karin kudin kashewar su na 2018, kuma sai ta ajiye shi ba tare da wani bayani ba.

DUBA WANNAN: An fasa gidan yarin masu aikata kisan kai a garin Minna

A shekarar da ta gabata, bayan tsananin takura daga masu ruwa da tsaki na kasar nan, shugabannin majalisar dokoki sun fitar da bayanin karin kudin su na kashewa, inda mutane da dama suka samu damar kalubalantar su.

A tsarin da shugaban kasan ya mikawa, mahukunta sun bawa majalisa naira biliyan 139.5 a matsayin tsarin kudin su.

Majiyar mu Legit.ng ta ruwaito cewa, kwanaki 18 bayan an mika tsarin kari kudin kashewar nasu na 2018, majalisar dattawan taki bada bayanin komai akan kasafin kudin, akasin abinda ya faru shekarar da ta gabata, wanda a ranar da aka mika tsarin suka bada bayanin.

A wata tataunawar waya, wani mahukunci yace, kafin a bada bayanin tsarin kashe kudin, sai an tabbatar da an duba tsarin 2017.

"Ba wai bayanin na shekarar nan bane, sai an duba yanda aka kashe na shekarar da ta gabata. Koda kuwa a zama na biyu ne, dole a tattauna. Sai bayan anyi hakan ne sannan maganar bayanin na wannan shekarar nan zata biyo baya."

Duk kokarin da manema labarai suka yi tayi wajen ji ta bakin mai magana da yawun majalisar dattawan, Aliyu Sabi Abdullahi (APC, Niger) abin yaci tura, domin kuwa baya daukan kiran waya.

Mai magana da yawun majalisar dokokin, Abdulrazak Namdas(APC, Adamawa) a lokacin da aka tuntube shi da zancen, yace bayanin tsarin kashe kudin na nan tafe.

"Bamu da bayanin yanzu, amma nan bada dadewa ba zamu fitar da shi."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel