Gasar cin kofin duniya: Kanu ya gamu da sharrin ‘yan fashi a kasar Rasha, sun sace masa miliyoyi

Gasar cin kofin duniya: Kanu ya gamu da sharrin ‘yan fashi a kasar Rasha, sun sace masa miliyoyi

An yashe tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Nwankwo Kanu a filin tashi da saukar jiragen sama na Sheremetyevo dake birnin Moscow ta Rasha yayin da ya sauka kasar domin buga wani wasan sada zumunta da FIFA ta gayyace shi.

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan fashi sun sace kudin kanu da yawan su ya Dalar Amurka $11,000 (Yuro 9,300).

Kanu ya gamu da sharrin ‘yan fashin ne bayan an canja masa jirgin da ya kawo shi daga kasar Ingila kamar yadda wata kafar yada labarai ta sanar.

Gasar cin kofin duniya: Kanu ya gamu da sharrin ‘yan fashi a kasar Rasha, sun sace masa miliyoyi

Kanu Nwankwo

Wata kafar watsa labarai (TASS) ta rawaito cewar, ‘yan sanda a kasar Rasha sun ce suna tsare da mutane biyu, dake aikin sauke kaya daga jirgi, da ake zargi da sacewa Kanu kudin sa.

Mun yi nasarar kwato kudin daga hannun barayin kuma bad a wani bata lokaci ba zamu mayar das u ga mai su,” kakakin ‘yan sanda Irina Volk ta sanar.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya lamuncewa sifeton 'yan sanda kama Saraki

Kanu ya buga was an da FIFA ta shiryawa tsofin gwarazon ‘yan was an kwallon kafa da aka buga da tsofin ‘yan was an kwallo na kasar Rasha a jiya, Lahadi. Bangaren su Kanu ya yi nasara a was an da aka tashi 6-4.

A kasar ta Rasha dai za a buga gasar wasannin cin kofin duniya da za a fara a watan nan, Yuni, da muke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel