Jarrabawar shiga jami’a: Nayo hayar wani ne saboda ‘dana – Uwa ta tona asiri

Jarrabawar shiga jami’a: Nayo hayar wani ne saboda ‘dana – Uwa ta tona asiri

Jami’an rundunar Nigerian Security and Civil Defence Corps dake jihar Nasarawa sun kama wata uwa, Misis Chika Okoye, danta Samuel da kuma abokinsa Dan Abah kan satar jarrabawa.

Chika ce ta yo hayar Abah domin ya rubuta jarrabawar shiga jami’a wanda aka kammala kwanan nan.

Matar mai shekaru 35 da ta amsa laifinta ta bayyana cewa tsawon shekaru da dama dan nata bai samu shiga jami’a ba ita kuma ta gaji da hakan kuma babu wanda ya taimake su.

A cewarta tana da sauran yara da suka kammala jami’a amma tsawon shekaru hudu kenan Samuel bai samu makaranta ba.

Jarrabawar shiga jami’a: Nayo hayar wani ne saboda ‘dana – Uwa ta tona asiri

Jarrabawar shiga jami’a: Nayo hayar wani ne saboda ‘dana – Uwa ta tona asiri

Saboda haka sai ta nemi abokin shi ya taimaka ya zana masa jarrabawar idan ya so sai ta ba shi wani abu.

KU KARANTA KUMA: Lallai auran mata da yawa akwai dadi – Wani Bahaushe ya yabi matansa guda 3 cikin shauki (hotuna)

Daga karshe ta roki ayi mata gafara cewa ta san hakan laifi ne.

Kwamandan NSCDC din, Mohammed Gidado-Fari yace an kama Abah yayinda yake rubuta jarrabawar a makarantar Command Secondary School, Lafia bayan anyo hayar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel