Taurin kai: NCS ta hana wani Jami’in da aka kora aiki da karfin tsiya kudin sa duk da umarnin Kotu

Taurin kai: NCS ta hana wani Jami’in da aka kora aiki da karfin tsiya kudin sa duk da umarnin Kotu

Mun samu labari daga Daily Trust cewa a karshen 2009 ne wani babban Jami’in Hukumar Kwastam Abdullahi Bello Gusau ya bankado wata badakala ta sama da Naira Biliyan 1.3a tashar Legas. Sai dai a dalilin haka ne aka kore sa daga aiki.

Taurin kai: NCS ta hana wani Jami’in da aka kora aiki da karfin tsiya kudin sa duk da umarnin Kotu

Hamid Ali yayi watsi da takardun Ministocin Buhari da umarnin Kotu

Bayan kwanaki kadan da Abdullahi Bello Gusau ya fallasa wannan cuwa-cuwa da ake yi a Tashar Apapa ne sai kwatsam ya ji labari cewa an kore sa daga aiki. Kafin nan dai sai da aka yi ta sakewa wa wannan Jami’u wurin aiki a gidan na Kwasatam.

Kafin nan dai AC Abdullahi Dikko Inde ya rubuta takarda inda yake yabawa Abdullahi Gusau da kokarin sa. Sai kuma ga labarin sallama daga aiki babu gaira-babu dalili. Sakamakon haka ne dai Jami’in ya sheka Kotu inda kuma yayi nasara a karshe.

KU KARANTA: DSS ta janye tsaron da ta ba Shugabannin Majalisar Tarayya

Da farko wani babban Kotu ta ba shi rashin gaskiya amma ko da ya koma Kotun daukaka kara yayi nasara aka kuma nemi a biya sa dul albashin da ya rasa a kuma maida sa ofis. Sai dai Hukumar Kwastam tayi watsi da wannan umarni na Kotu.

A lokacin Dikko Inde an dai maida Abdullahi Gusau ofis ne kurum na watanni 6 kuma daga baya aka tsaida albashin sa gaba daya. Hakan ya sa don dole ya ruga Kotun Koli inda ya nemi a fito masa da hakkin sa kuma Ministocin kasar 2 su ka sa baki.

Fiye da shekara guda kenan da Kotun Koli ta ba wannan tsohon Jami’i na Kwastam gaskiya amma Shugaban NCS na yanzu Hamid Ali bai bi umarnin ta ba. Haka kuma Ministar kudi da Ministan shari’a sun aikawa Ali wasika amma yayi kunnen kashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel