Ku Godewa Allah da ya baku Buhari a matsayin shugaban kasa – cewar wani babban Malami

Ku Godewa Allah da ya baku Buhari a matsayin shugaban kasa – cewar wani babban Malami

- Batun sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara sauyawa zuwa yabo

- Wani babban Malami ya shawarci 'yan Najeriya da kada su zama tamkar kaza mai ci ta goge bakinta

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Buharin ke fuskantar zazzafar suka daga bangarorin Malaman addini

Wani babban Malamin addinin Kirista Rev. Raphael Ogunkunle a jihar Kaduna ya ce kamata yayi ‘yan Najeriya su godewa Allah bisa albarkar da yayi musu na samun Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa.

Kamata yayi ku godewa Allah da ya baku Buhari a matsayin shugaban kasa – cewar wani babban Malami

Kamata yayi ku godewa Allah da ya baku Buhari a matsayin shugaban kasa – cewar wani babban Malami

Ogunkunle yayi wannan maganar ne a jiya Lahadi yayin babban taron jawabi da godiya karo na 10 da kuma kaddamar da tarihin wurin bautar ta su.

Ya ce, samun Gwamnatin Buhari wani nufi ne na Ubangiji kuma ita ce wadda tafi kowacce Gwamnati dacewa da Najeriya.

A cewarsa maimakon ala-wadai da ake yiwa Gwamnatin, kamata yayi ‘yan Najeriya su rika yin godiya bisa irin nasarorin da aka samu tun bayan hawan Buhari Mulki, sannan sai su zuba ido da tsammanin kara samun wasu cigaban.

Sannan ya bayyana cewa duk wasu abubuwan rashin jin dadi da yake faruwa na kalubale da ake fuskanta yana wanzuwa ne sakamakon irin tofin ala-tsine da ‘yan Najeriyan ke yi.

A don haka Malamin ya tsame kansa daga cikin rukunin masu aibata Gwamnatin shugaba Buharin, kana ya shawarci ‘yan Najeriyar da sui ya bakinsu, tare da yin addu’o’in samun sauki.

A nasa jawabin babban bako mai jawabi Pasto Olatunde Ogunbiyi cewa yayi, ‘yan Najeriya suna dalilai masu yawan gaske da ya kamata su godewa Allah bisa albarkar da yayi musu na raya Najeriya ta kawo har ya zuwa yanzu.

Ogunbiyi ya kuma tabbatar da cewa Ubangiji ya na karawa duk zuciyar da take gode masa, a saboda haka ya kamata kowa ya koyi godewa ni’i’mominsa domin rabauta da falalarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel