Jami’an Yansanda sun cika hannu da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane (Hoto)

Jami’an Yansanda sun cika hannu da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane (Hoto)

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya, reshen jihar Osun sun samu nasarar damko wuyar wasu gagararrun yan fashi da makami da suka shahara wajen satar mutane, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansandan sun bayyana sunayen barayin mutanen kamar haka – Henry Omenihu mai shekaru 24, Paul Chituru shima 24 da kuma Henry Bright mai shekaru 18, kuma an kama su ne da hannun cikin satar wani shugaban direbobin jihar, Kayode Agbeganji da matarsa, Oyeyemi.

KU KARANTA: Wani dan majalisa ya sanya tukuicin N5,000,000 ga duk wanda ya yanko masa gashin Shehu Sani

Jami’an Yansanda sun cika hannu da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane (Hoto)

Gagga gaggan masu garkuwa da mutane (Hoto)

Majiyarta ruwaito Kwamishinan Yansandan jihar, Fimihan Adeoye yana fadin cewa sun kama miyagun mutanen ne a unguwar Osu dake cikin karamar hukumar Atakumosa ta yamma a ranar 29 ga watan Mayu, inda ya kara da cewa a ranar 14 ga watan Afrilu suka sace Kayode da matarsa, inda suka sako su a jihar Kros Ribas bayan an biyasu kudin fansa.

Daga karshe Kwamishina Fimihan ya bayyana cewar zasu gurfanar dasu a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike, sa’annan ya yi kira ga jama’a dasu taimaka ma yansanda da muhimman bayanai kan miyagun mutane a duk inda suke.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel