'Barayin Mai sun shiga Uku domin zamu toshe musu duk wata kofar numfashi – Sojojin Ruwa

'Barayin Mai sun shiga Uku domin zamu toshe musu duk wata kofar numfashi – Sojojin Ruwa

- Sojoji sun yi hubbasa a wani yunkuri na dakile yawaitar ta'addancin barayin danyan mai

- Sai dai Jami'an Rundunar sun nemi hadin kan Mutanen yankin domin cimma nasara tare

- Akan yawaita samun rahotan aika-aikar barayin danyan man a jahohin dake da arzikin man fetir din

Sojojin Ruwan Najeriya sun aike da wani sakon gargadi ga barayi masu satar a Teku a yankin Niger Delta da su tuba tun lokaci bai kure ba domin Rundunar ta shirya yin mganinsu.

Kwamandan Jirgin NNS Delta Ibrahim Dewu ne yayi wannan gargadin a garin Warri na jihar Delta, ya ce Sojojin Ruwan na cigaba da daukar matakan tabbatar da dakile barayin man da kuma barayin kan Tekua a yankin.

'Barayin Mai sun shiga Uku domin zamu toshe musu duk wata kofar numfashi – Sojojin Ruwa

'Barayin Mai sun shiga Uku domin zamu toshe musu duk wata kofar numfashi – Sojojin Ruwa

A ranar 31 ga watan Janairu wannan shekara ne dai Rundunar NNS Delta ta cafke wani Jirgi da yake dauke da lita 386,000 na danyan mai, tare da Mutane Tara da suke cikinsa. Kuma tuni har sun mika su ga hukumar EFCC.

KU KARANTA: An gano rishon Biliyan 9 da Jonathan ya saya bayan shekaru 3

A don haka ne yayi kira da samun hadin kai domin yin aiki tare tsakanin Sojojin da kuma Mutanen Jihar don a hada hannu a magance aiyukan tsagerun a yankin gami da tabbatar da tsaro baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel